Isa ga babban shafi
Turai

Kungiyar tarayyar turai na neman kama masu safarar bakin haure su kimanin dubu 65

Mahukumtan kungiyar tarayyar Turai na neman kimanin masu safarar bakin haure zuwa nahiyar su dubu 65, adadin da ya rubanya sau biyu a cikin shekaru 3 da matsalar kwararar bakin hauren ta ta’azara a nahiyar.

shugaban Europol Bob Wainwright
shugaban Europol Bob Wainwright World Economic Forum (www.weforum.org)/Photo by Heinz Tesarek
Talla

Duk da nasarar da aka samu ta raguwar yawan bakin hauren dake yi nasarar kutsa kai a nahiyar turai ta tekun Medetaraniyan a 2016, har yanzu matsalar masu tsallakar da bakin na nan daram, kamar yadda hukmar yaki da masu fasa kwabrin bakin haure ta turai ta sanar.

A binciken da mahukumtan kasashen turan suka bada umarnin gabatarwa, ya nuna cewa, yanzu haka sannu a hanakli na ci gaba da tantance masu aikata wannan laifi

Robert Crepinko, shugaban sashen dake kula da shige da ficen baki na nahiyar turai ya sanar da AFP cewa, a karshen shekarar da ta gabata suna da sunayen kimanin masu safarar bakin hauren zuwa turai dubu 65 akan girgam

A shekara ta 2015 yawan masu wannan aiki na laifi su dubu 30 ne, kafin su zama dubu 55 a 2016, a yayin da a bara 2017 yawansu ya karu da dubu 10 inda ajimilce yau yawan nasu ya kai dubu 65.

Kimanin 63% na mutanen da hukumar yan sandan ta Europol ta tantance yan asalin nahiyar ta turai mafi yawansu kuma daga yankin Balkans, 14% yan yankin gabas ta tsakkiya, 13% yan Afrika, 9% daga yammacin Asiya, sai kuma 1% daga yankin latin Améruka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.