Isa ga babban shafi
Rasha-Birtaniya

Rasha na fatan sake ganawa da Birtaniya

Jakadan Rasha a Birtaniya Akexandre Iakovenkho ya bukaci ganawa da ministan harakokin wajen Birtaniya Borris Johnson domin sake duba dangatakar dake da kwai tsakanin kasashen biyu.

Jami'an Birtaniya masu binciken dangane da  yukunrin kisan Skripal da guba  a Birtaniya
Jami'an Birtaniya masu binciken dangane da yukunrin kisan Skripal da guba a Birtaniya REUTERS/Hannah McKay
Talla

Jakadan na Rasha ya bayyana cewa wannan ganawa idan har ta samu zata taimakawa domin sake duba wasu daga cikin matsalloli dake hana ruwa gudu tun bayan da Birtaniya da wasu kasashen duniya suka zargi Rasha da kokarin kashe tsohon jami’in ta Skripal da yar’ sa Joulia a yankin Salisbourg dake kudu maso yammacin Birtaniya ranar 4 ga watan Maris na wannan shekara.

Rasha na sa ran Birtaniya za ta yi naam da wannan tayi da ta share kusan makonni uku ta na kokarin ganin an yi wannan ganawa tsakanin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.