Isa ga babban shafi
Diflomasiya

Rasha zata sake korar jami'an diflomasiyyar Birtaniya

Rasha ta ce tilas Birtaniya ta sake rage adadin jami’an diflomasiyarta sama da 50 daga kasar, kari kan 23 da gwamnatin Rashan ta iza keyarsu gida da farko.

Hedikwatar ma'aikatar harkokin wajen Rasha da ke birnin Moscow.
Hedikwatar ma'aikatar harkokin wajen Rasha da ke birnin Moscow. REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Matakin ya zo dai dai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke dada yin tsami, akan sanyawa tsohon dan leken asirin Rasha guba tare da ‘Yarsa a gidansu da ke Ingila.

Rasha ta kuma bukaci Birtaniya ta yi Karin bayani akan dalilan da yasa aka yi wa wani jirgin fasinjanta da ya sauka a kasar binciken kwakwaf, inda ta ce itama tana da ikon aikata hakan akan jiragen saman Birtaniya da ke safara zuwa kasar.

Matakin na Rasha ya shafi kasar Faransa, inda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce Rashan ta kori jami’an diflomasiyyarta 4, a matsayin martani kan marawa Birtaniya baya da ta yi, wajen korar wasu jami’an diflomasiyar Rashan, bisa zarginta da ake da hannu, wajen kokarin hallaka tsohon dan leken asirinta Sergie Skrippal da  ‘yarsa Yulia a gidansu da ke Ingila ta hanyar amfani da guba.

Zuwa yanzu Rasha ta kori jami’an Diflomasiyya da dama daga kasashe 23 a matsayin raddi kan marawa Birtaniya baya da suka yi.

Daga cikin kasashen da korar ta shafa akwai Jamus, Canada, Poland da kuma Sweden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.