Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta kara haraji kan robobin da ba a sake sarrafawa

Kasar Faransa na shirin gabatar da dokar da za ta kara yawan haraji kan kayan da ake sanya su cikin robar da ba a iya sake amfani da su.

Faransa ta kaddamar da shirin kawo karshen amfani da robobin da ba a iya sake sarrafawa.
Faransa ta kaddamar da shirin kawo karshen amfani da robobin da ba a iya sake sarrafawa. ©Reuters
Talla

Matakin bangare ne na shirin da kasar ke yi na ganin cewa daga shekarar 2025, robar da za a iya sake sarrafa su ne kawai za a dinga mu’amala da su a fadin kasar.

Sakatariyar Kula da Muhalli na Faransa, Brune Poirson ta ce, matakin na daga cikin jerin matakan da za su dauka a shekaru masu zuwa domin kawo karshen yadda ake zubar da robobi.

Jami’ar ta ce, kaddamar da yaki kan robobi kawai bai isa ba, ya zama dole a kara da yadda za a bunkasa tattalin arzikin Faransa da kuma sanya wata doka da mutane za su dinga karbar wasu kudade daga kayan da suka saya cikin roba, idan sun killace su.

Poirson ta ce, a karkashin dokar, kayyakin da ake sa su cikin robar da za a iya sake sarrafa zasu samu ragin kashi 10, yayin da wadanda ake sanya su cikin robar da ba za’a iya sake sarrafawa ba zasu samu Karin harajin kashi 10.

Gwamnatin Faransa na kuma wani yunkuri na kara harajin birne shara a filaye, da kuma zabtare haraji kan kan kayan da ake iya sake amfani da su, domin magance tarin robobin da suka addabi jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.