Isa ga babban shafi
Faransa

Dokar haramta sanya nikabi ta janyo cece-kuce a Faransa

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka kan dokar Faransa na haramta rufe fuska baki daya da nikabi ga mabiya addinin Islama.Acewar kwamitin majalisar kan hukuncin na Faransa, matakin haramta sanya Nikabin ga mata musulmi yunkuri ne na take hakkin wata al’umma inda ya bukaci gaggauta nazartarsa.

Sanarwar kwamitin kare hakkin dan na Majalisar Dinkin Duniya cikin sanarwarsa ta yau Talata ya ce kai tsaye hukuncin zai tauye hakkin miliyoyin mata da ke kokarin bin dokokin addininsu na Islama.
Sanarwar kwamitin kare hakkin dan na Majalisar Dinkin Duniya cikin sanarwarsa ta yau Talata ya ce kai tsaye hukuncin zai tauye hakkin miliyoyin mata da ke kokarin bin dokokin addininsu na Islama. REUTERS/Charles Platiau/File Photo
Talla

Kwamitin wanda ya bai wa Faransa wa’adin kwanaki 180 don gabatar da hujjojin da suka sanya su kakaba dokar wadda kwamitin ya yi ikirarin cewa kasar ba ta da hujja kan dokar wadda ta gaza samun karbuwa hatta a wasu kotunan kasar.

A cewar kwamitin har yanzu ya gaza gamsuwa da hujjar farko wadda faransa ta togace da ita kan cewa hukuncin na da nufin rage ayyukan ta’addanci a kasar tare da tabbatar da tsaro.

Batun wanda akalla fitattun lauyoyi 18 masu zaman kansu daga kasashen duniya ke kare shi baya ga masu fafatukar kare hakkin dan adam dama masu faftukar tabbatar da daidaito a addinai da siyasa kawo yanzu Faransar ta gaza bayar da hujja kan hukuncin.

Ko a shekarun 2008 da 2014, ma kotun kare hakkin dan adam ta kungiyar tarayyar Turai ta zartas da wani hukuncin da ke nuna cewa haramcin amfani da nikabin wajen rufa fuska baki daya da mabiya addinin islama ke yi bai sabawa ‘yancin gudanar da addini ba, ko da dai dama tun a wancan lokaci da dama basu yi amanna da hukuncin ba.

Sai dai sanarwar kwamitin kare hakkin dan na Majalisar Dinkin Duniya cikin sanarwarsa ta yau Talata ya ce kai tsaye hukuncin zai tauye hakkin miliyoyin mata da ke kokarin bin dokokin addininsu na Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.