Isa ga babban shafi
Faransa-Birtaniya

'Yan Birtaniya da ke neman mafaka a Faransa sun karu

Ma'aikatar Cikin Gidan Faransa ta ce, an samu karuwa sosai na yawan 'yan kasar Birtaniya da ke neman zama a kasar Faransa, shekara guda kafin kasar ta fice daga cikin Kungiyar Kasashen Turai. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke takun saka da kungiyar Turai wajen ganin an raba gari ba tare da samun tashin hankali ba.

Wasu 'yan Birtaniya da ke tattakin nuna adawa da ficewar Birtaniya daga Turai
Wasu 'yan Birtaniya da ke tattakin nuna adawa da ficewar Birtaniya daga Turai REUTERS/Henry Nicholls
Talla

Alkaluman da ma’aikatar ta gabatar sun bayyana cewar, a shekarar 2015 'yan Birtaniya 386 suka nemi takardar zama 'yan Faransa, amma adadin ya tashi zuwa 3,173 a bara, yayin da a cikin watanni 6 na wannan shekara kawai aka samu mutane 1,370 da suka gabatar da bukatar su.

A karkashin dokar kungiyar kasashen Turai, 'yan kasar Birtaniya na da hurumin zama da kuma gudanar da aiki a kowacce kasa ba tare da wata tsangwama ba, amma da zaran kasar ta fice daga kungiyar, 'yan kasarta sun zama baki a sauran kasashen Turai, kamar yadda bako ke zuwa yankin daga sassan duniya.

Ya zuwa yanzu dai tattaunawar raba hannun riga tsakanin bangarorin biyu na tafiyar hawainiya, in da kowanne bangaren ke zargin dayan da haifar da matsala.

Tuni gwamnatin Faransa ta shirya wata dokar da za ta bata damar duba matsayin 'yan Birtaniya dubu 150 zuwa 300 da ke zama a cikin kasar, wadanda akasarinsu sun yi ritaya daga aiki, amma kuma suna zama a yankunan karkara.

Har ila yau kungiyar na dibar sabbin ma’aikatan da za su yi aiki akan iyakokin kasashen da zaran Birtaniya ta fice daga kungiyar.

Ficewar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai za ta mayar da 'yan kasar baki a duk kasashen da za su tafi da ke yankin na Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.