Isa ga babban shafi
EU-Birtaniya

EU za ta mutunta yarjejeniyarta da Birtaniya bayan ficewa

Babban Jami’in da ke Kula da ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayar Turai Michel Barnier ya ce, kungiyar za ta mutunta yarjeniyoyin da ta kulla da kasar bayan ficewarta daga Turai.

Michel Barnier da ke Kula da Ficewar Birtaniya daga Turai
Michel Barnier da ke Kula da Ficewar Birtaniya daga Turai EUTERS/Francois Lenoir
Talla

Barnier wanda ke tare da Ministan Harkokin Waje na Jamus Heiko Maas a wani taron manema labarai a birnin Berlin ya ce, Kungiyar Tarayar Turai na cikin shiri don ganin dorewar dukkanin yarjeniyoyin da suka kulla.

Barnier ya ce, zumunci zai daure tsakanin bangarorin biyu musamman ta fannin cinikayya da kasuwanci da sufurin jiragen sama da tsaro da kuma tsarin hulda da kasashen duniya.

Jami'in ya ce, za a tabbatar cewa ba a kauce daga sharuddan yarjeniyoyin da bangarorin biyu suka kulla ba wadda ta kunshi ginshikai 4 da suka hada da kasuwancin-bai-daya da ‘yancin zirga-zirga da safarar kayayyaki da sauran harkokin yau da kullum.

Duk da cewa watanni 7 suka rage kafin a hukumance Birtaniya ta yi bankwana da kungiyar, amma tattaunawa tsakaninsu na tafiyar hawainiya game da sharuddan da aka gindaya.

A makon jiya Ministan Kudi na Britaniya Philip Hammond ke cewa, ficewar kasar ba tare da hakikanin yarjejeniya ba na da hadari, kasancewar ranar 29 ga watan 3 na badi ne ake dakon ganin ficewar idan komi ya tafi yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.