Isa ga babban shafi
Faransa

Masu zanga-zanga a Faransa sun katse ganawar Minista a Reunion

Dubban masu zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a Faransa sun kawo tsaiko a wata ganawar ministan yankunan kasar da ke ketare Annick Girardin da jagororinsu, bayan kururuwar da suka rika yi tare da neman lallai shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi murabus.

Yankin Reunion na daga cikin matalautan yankin da ke karkashin ikon kasar ta Faransa, inda dubban jama'a suka shafe tsawon makwanni 2 suna gudanar da zanga-zangar adawa da shirin na Emmanuel Macron.
Yankin Reunion na daga cikin matalautan yankin da ke karkashin ikon kasar ta Faransa, inda dubban jama'a suka shafe tsawon makwanni 2 suna gudanar da zanga-zangar adawa da shirin na Emmanuel Macron. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Annick Girardin ministan da ke kula da yankunan Faransa na kasashen ketare, a ziyarar da ya ke a tsibirin Reunion don sasantawa da jagororin masu zanga-zangar adawa da Farashin man fetur a kasar, dubban masu zanga-zangar sun nuna rashin amincewa da ganawar matakin da ya tilasta masa katse tattaunawar tare da komawa birnin Paris.

Akalla mutane dubu 800 suka bazu a titinan yankin rike da kwalaye da ke neman murabus din shugaban ko kuma samar da gyara a shirin na kara farashin man fetur da dangoginsa wanda a cewarsu ke kara tsananai ga marasa karfi.

Shugaba Emmanuel Macron a makon jiya ya ce zai dauka matakan da suka dace don magance matsalar tsadar rayuwa bayan arangama tsakanin jami’an tsraro da masu zanga-zangar a gab da fadar Elysee ko da dai ya ce yana kan bakarsa na kara haraji kan kamfanonin wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen gurbata muhallai nan da watan Janairun sabuwar shekara.

Zanga-zangar dai tafi tsananta a Reunion yankin da ake ganin ya fi yawan matalauta a Faransa, matakin da ya sanya ministan tattaki don sulhuntawa da jagororinsu ko da dai abin ya ci tura bayan boren da ya fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.