Za mu kawo karshen zanga-zanga a Faransa
Shugaban Faransa Emmanuel Macron dake jawabi a taron Argentina taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya ya bayyana cewa ba zai amince a ci gaba da tayar da tarzoma a kasar Faransa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Macron na jawabi ne a dai-dai lokacin masu zanga-zanga ke ci gaba da karo da jami’an tsaro a birnin Paris da wasu sassan kasar na Faransa.
Fadar Firaministan kasar ta sanar da cewa yan sanda suna tsare da masu zanga-zanga kusan 500,yayinda aka bayyana cewa wasu yan Sanda sun samu rauni.
Firaminista Edouard Philippe ya bukaci ganawa da wakilan masu bore,sai da hakan ya citura
Shugaba Macron a fusace ya nuna matukar damuwa tareda jadadda cewa doka zata yi aiki domin tabbatar da doka da oda a ilahirin kasar ta Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu