Isa ga babban shafi
Faransa

Za a haramta zanga-zanga a Faransa

Firaministan Faransa, Edouard Philippe ya sanar da shirin gwamnatin kasar na haramta zanga-zangar da ta saba ka’ida, yayin da mahukuntan kasar ke ci gaba da fafutukar kawo karshen zanga-zangar masu sanye da riguna launin dorawa.

Firaministan Faransa, Edouard Philippe
Firaministan Faransa, Edouard Philippe ERIC FEFERBERG / POOL / AF
Talla

Wannan na zuwa ne bayan wasu kusoshi biyu na jam’iyya mai mulkin Italiya sun bayyana goyon baya ga masu zanga-zangar , suna masu zargin gwamnatin Faransa da nuna halin-ko-in-kula ga talakawan kasar.

Mataimakin Firaministan Italiya, Luigi Di Maio ya caccaki gwamnatin Faransa saboda kare muradun masu hannu da shuni da ‘yan alfarma da ya ce tana yi, kamar yadda takwaransa, Matteo Salvini wanda shi ma ya goyi bayan masu zanga zangar ya yi.

Salvini, ya fito karara yana cewa, shugaba Emmanuel Macron ya yi watsi da talakawan Faransa a gefe saboda haka dole ne a kowanne lokaci ya goyi bayan zanga-zanga daga al’ummar da shugabanta ya yi biris da ita.

Shi ma Di Maio ya bai wa Faransawa masu zanga-zanga damar amfani da dandalin sadarwar jam’iyyarsu ta Rouseau don inganta shirinsu tare da tsara jadawalin zabe.

Kimanin masu zanga-zangar dubu 50 ne suka bazama kan titunan Faransa a ranar Asabar don adawa da manufofin gwamnatin shugaba Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.