Isa ga babban shafi
Turai-Amurka

EU ta wallafa sabbin tsare-tsaren kasuwanci da Amurka

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta wallafa tsarin aiwatar da yarjejeniyar cinikayyar bai daya tsakaninta da Amurka a wani mataki na kawo karshen yakin kasuwancin da su ke fuskanta da shugaban kasar Donald Trump.

Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk.
Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk. JOHN THYS / AFP
Talla

A cewar shugabar sashen cinikayya ta kungiyar Tarayyar Turai Cecilia Malmstrom, yarjeniyoyin na cikin tsare-tsaren da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a bara bayan da Amurkan ta kara haraji kan kayakin karafa da samfolo da ake shigar mata daga kasashen Turai.

Ka zalika matakin bijirowa tare da samar da gyare-gyare a yarjeniyoyin wani yunkuri ne na hana Donald Trump kara haraji kan motocin da Turai ke shigarwa Amurkan musamman dai dai lokacin da tarin motocin Jamus ke shirin shiga kasar.

Cecilia Malmstrom ta ce ba wai su na neman sassauci a harajin Trump kan kayakin abinci da ya kara ba ne sai dai suna so kada harajin ya shafi cinikayyyar Motoci.

A makon jiya ne Trump ya fitar da jadawalin haraji kan kayakin abincin da ke shiga Amurkan daga Turai, matakin da kungiyar ta ce bata kalubalantarsa sai dai za ta fitar da na ta tsare-tsaren.

Yanzu haka dai kunshin yarjejeniyar EU ta rarraba shi ga kasashe mambobinta 28 wanda kuma sai sun amince ne kafin ta fara tattaunawa da Amurka don fahimtar juna gabanin daukar mataki na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.