Kankarar tsaunukan Himalaya ka iya narkewa nan da wasu shekaru
Wani binciken masana ya nuna cewar kashi biyu bisa uku na Yankin duniya da ake kira tsaunukan Himalaya da ke fama da tsananin sanyi na iya narkewa nan da shekarar 2100 muddin ba’a magance matsalar sauyin yanayin da ake samu ba.
Wallafawa ranar:
Masanan kimiyan sun ce, ko da an aiwatar da yarjejeniyar Paris ta rage dumamar yanayin da ake samu na maki daya da rabi, kashi daya bisa uku na Yankin Himalaya zai narke.
Rahotan binciken ya ce Yankin na samarwa akalla mutane sama da miliyan 250 ruwan sha da kuma wasu sama da biliyan daya da rabi da ke amfana da ruwan da su ke samu a tafkuna.
Masanan sun ce wasu manyan tafkuna 10 da ake da su a duniya duk suna samun ruwan su ne daga wannan yankin cikin su har da Ganges da Indus da Yellow da Mekong da Irrawaddy.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu