Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

May za ta gana da Juncker na EU kan yarjejeniyar ficewar Birtaniya

Ana saran Firaministar Birtaniya Theresa May ta gana da shugaban kungiyar kasashen Turai Jean Claude Juncker yau Talata a yunkurin da take na shawo kan kungiyar domin sake tattauna yarjejeniyar ficewa daga kungiyar.

Matukar EU ta gaza yiwa yarjejeniyar ta Birtaniya kwaskwarima, kasar na da zabin ko dai ta fice daga EU ba tare da yarjejeniya ba, ko kuma ta hakura da shirin ficewar
Matukar EU ta gaza yiwa yarjejeniyar ta Birtaniya kwaskwarima, kasar na da zabin ko dai ta fice daga EU ba tare da yarjejeniya ba, ko kuma ta hakura da shirin ficewar UK Parliament/Jessica Taylor/Handout via REUTERS
Talla

Theresa May dai na kokarin ganin kungiyar ta EU ta yiwa yarjejeniyar da suka cimma kwaskwarima tun bayan da Majalisar kasar ta yi watsi da ita a watan jiya.

Za a iya cewa Firaministar ta Birtaniya na cikin tsaka mai wuya la'akari da yadda tun a baya EU da sauran shugabannin kasashen kungiyar 27 suka ja daga kan cewa baza su sake bude babin yarjejeniyar ta su da Birtaniya ba.

Mai magan da yawun Juncker, Margaritis Schinas ta ce matsayin kungiyar Turai a bayyana ya ke, sai dai sun zuba ido suga abinda May za ta je da shi.

Matukar dai EU ta ki amincewa da yiwa yarjejeniyar Kwaskwarima, ya zama kenan Theresa May na da zabin ko dai ta fice daga EU ba tare da yarjejeniya ba, ko kuma ta ajje shirin ficewar dungurugum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.