Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

EU a shirye ta ke ta karawa Birtaniya wa'adin ficewa - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kungiyar Turai a shirye ta ke ta bai wa Birtaniya wani Karin lokaci na wucin gadi domin ganin ta kulla yarjejeniyar ficewa daga cikin ta bayan wa’adin 29 ga watan Maris da aka gindaya.

Yanzu haka dai kungiyar ta EU na duba yiwuwar karawa Birtaniyar lokaci sai dai bisa sharadin sai ta bayyana gamsassun dalilai da ke nuna bukatar hakan
Yanzu haka dai kungiyar ta EU na duba yiwuwar karawa Birtaniyar lokaci sai dai bisa sharadin sai ta bayyana gamsassun dalilai da ke nuna bukatar hakan REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Da ya ke karbar bakoncin shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel a fadar Elysee da ke birnin Paris Shugaba Macron ya ce yanzu haka suna nazari kan bukatar da Birtaniya ta gabatar na son kara mata lokacin raba garin tsakanita da kungiyar Tarayyar Turai.

A cewar Emmanuel Macron akwai yiwuwar su sake komawa tattaunawa kan yarjejeniyar farko da Theresa May ta kulla da kasashen na EU dangane da ficewar, yarjejeniyar da ta gaza samun karbuwa a Majalisar Birtaniyar.

Kalaman na Macron dai na zuwa ne dai dai lokacin da Theresa May ke neman Majalisar Birtaniya ta amince da kara mata lokacin ci gaba da tattaunawar ficewar kasar daga tarayyar Turai tare da fayace masu irin matakan da ta ke shirin dauka matukar aka gaza cimma jituwa a tsakaninsu.

A bangaren guda jagoran shirin ficewar Birtaniyar daga EU Michel Barnier, ya  bayyana yiyuwar kara lokacin raba garin tsakanin EU da Birtaniyar, sai dai bisa sharadin sai Birtaniya ta bayyana gamsassun dalilai kan bukatar kara lokacin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.