Isa ga babban shafi
Faransa

Masu zanga-zanga sun haddasa hadura a Faransa

Hukumar Kiyaye Hadura a Faransa, ta zargi masu zanga zangar nan da ke sanye da taguwa masu ruwan dorawa, wato ‘Yellow vests’ protesters’ da haddasa karuwar hadura na ababen hawa a kan hanyoyin kasar da kashi 17 a watan da ya gabata, sakamakon lalata na’urorin kiyaye hadura da suka yi.

Wasu masu rigunar dorawa da ke zanga - zangar adawa da Macron
Wasu masu rigunar dorawa da ke zanga - zangar adawa da Macron RFI/Mike Woods
Talla

A watan Fabrairu, mutane 253 ne suka mutu a kwaryar Faransa, wadda hakan ke nufin an samu karuwa na fiye da 37 a daidai irin wannan watan a shekarar da ta gabata.

An fara wannan zanga zangar a wajen Faransa ne a tsakiyar watan Nuwambar shekarar da ta gabata sakamakon Karin farashin man fetur, daga nan ne ta rikide zuwa bore na adawa da manufofin tattalin arziki da shugaba Emmanuel Macron ya bijiro da su, wanda suka ce an yi su ne don masu hannu da shuni da mazauna birane.

Tun daga lokacin ne masu zanga-zangar suka lalata daruruwan na’urorin kula da haddura da na kayyade gudun ababen hawa, suna zargin gwamnatin Faransa da takura wa mazauna kauyuka da suka dogara kacokan ga motoci ta wajen kayyade iya gudun motoci a kan hanyoyi zuwa kilomita 80 a sa’a daya daga 90.

Yayin da tuni aka rage yawan lalata na’urorin, a Alhamis din nan wakilin gwamnati kan abin da ya shafi hukumar kiyaye hadura, Emmanuel Barbe, yayi kashedin cewa matuka motoci na yin gudun fitar hankali, wanda hakan ya zama abin damuwa ainun.

Yayi kiyasin cewa za a kashe  Yuro miliyan 40 wajen gyaran na’urorin, sannan an tafka asarar yuro miliyan dari 5 na kudaden tarar da ake ci wa masu gudu fiye da kima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.