Isa ga babban shafi
Amurka

Trump yayi barazanar rufe kan iyakar Amurka da Mexico

Shugaban Amurka Donald Trump, yayi barazanar rufe kan iyakar kasar da Mexico ta yankin kudanci, nan da mako daya, muddin gwamnatin Mexico ta ki dakatar da kwararar ‘yan ci rani marasa takardun izini cikin Amurka ta kan iyakar.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Joshua Roberts
Talla

A watan Disamba da ya gabata, Trump yayi gargadin rufe baki daya kan iyakar Amurka da Mexico idan majalisun dokoki suka ki amsa bukatarsa ta kashe dala biliyan 5 da doriya, don gina Katanga tsakaninsu da Mexico.

Sai dai a waccan lokacin, maimakon rufe kan iyakar, sai ya dakatar da ayyukan wasu muhimman ma’aikatun kasar na tsawon kwanaki 35, lamarin da ya shafi ma’aikata kusan miliyan 1.

Gurguncewar da ayyukan ma’aikatun gwamnatin na Amurka su ka yi na wucin gadi a waccan lokacin, ya zama mafi tsawo da aka taba gani a Tarihin kasar.

Rabon da irin wannan mataki na dakatar da ayyukan muhimmai daga ma’aikatun Amurka ya auku, a dalilin sabanin Majalisar da bangaren zartaswa, tun a shekarar 1995 zuwa 1996, a zamanin mulkin Bill Clinton, lokacin da ma’aikatun suka shafe kwanaki 21 suna cikin yanayi na dakatar da ayyukansu na wucin gadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.