Isa ga babban shafi
Spain-Zabe

Jam'iyyar gurguzu za ta jagoranci kafa gwamnati a Spain

Karon farko a cikin shekaru sama da 40, jam’iyyar masu tsatsauran ra'ayi ta yi nasarar lashe kujeru da dama a zaben 'yan majalisar dokokin kasar Spain da aka gudanar jiya lahadi, to sai dai jam'iyyar ‘yan gurguzu da ke karagar mulki ce za ta sake kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Dan takarar Jam'iyar masu tsattsauran ra'ayi ta VOX Santiago Abascal bayan kada kuri'arsa a zaben 'yan Majalisu na Spain
Dan takarar Jam'iyar masu tsattsauran ra'ayi ta VOX Santiago Abascal bayan kada kuri'arsa a zaben 'yan Majalisu na Spain REUTERS/Susana Vera
Talla

Duk da cewa jam'iyyar PSOE ta Firaminista mai ci Pedro Sanchez ta samu kujeru 123 a majalisar dokokin mai wakilai 350, to amma ba za ta iya kafa sabuwar gwamnati ba sai ta kulla kawance da wasu jam'iyyun da take dasawa da su.

Jam,iyyar PP ce ta zo a matsayin ta biyu da kujeru 65, yayin da Ciudadanos ta ‘yan jari huja wadda aka yi hasashen cewa za ta iya bayar da mamaki, da kyar ta samun kujeru 60 a wannan zabe.

Karon farko tun bayan mutuwar dan kama karya Francisco Franco a 1975, masu zazzafen ra'ayi daga jam’iyyar VOX sun yi nasarar samun sake komawa zauren majalisar dokokin kasar da wakilai 24, duk da cewa shugabannin jam'iyyar sun yi hasashen samun kujeru 70 ne.

A can kuwa yankin Catalonia, shugabannin ‘yan aware biyar ne suka lashe kujerunsu duk cewa suna suna ne tsare a gidan yari

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.