Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan sandan Faransa na kama masu shirin kai wa kasar hari

‘Yan sandan Faransa sun cafke wani matashi dan shekara 16 a gabashin birnin Strasbourg, a ci gaba da binciken da suke yi game da zargin harin da aka shirya kaddamarwa kan jami’an tsaro da fadar shugaban kasar.

Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Faransa
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Faransa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Kame wannan matashi na zuwa ne bayan an cafke wasu mutune hudu a ranar 26 ga watan Afrilu dangane da shirin kaddamar da harin da  Ministan Harkokin Cikin Gidan Faransa, Chritophe Castaner ya ce, da ya kasance harin ta’addanci mafi muni a ‘yan tsakanin nan.

Ana zargin mutanen da  shirin kai harin a rana guda da fara azumin watan Ramadan na bana.

Rahotanni sun ce, matashin da  'yan sandan suka kama a baya-bayan nan, dalibin makarantar sakanbdare ne  kuma dan asalin Chechniya.

Bayanan sirri sun ce, matashin na gab da wallafa wani hoton bidiyon da ke nuna  mubaya’arsa ga kungiyar IS, zargin da majiyoyin bangaren shari’a suka tabbatar.

Tun a shekarar 2015 Faransa ta kasance cikin shirin ko ta kwana, bayan da hare- haren ta’addancin cikin gida suka lakume fiye da rayuka 250.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.