Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta wanke tsoffin ministocin kasar

Kotu a Faransa, ta wanke tsoffin ministocin kasar uku, da ake zargin cewa su ne suka bayar da umurnin sakin sojin hayar da suka kai hari kan barikin sojin kasar ta Faransa da ke birnin Bouake na kasar Cote d’Ivoire.

Michèle Alliot-Marie guda cikin ministocin da kotun ta wanke a yau
Michèle Alliot-Marie guda cikin ministocin da kotun ta wanke a yau Reuters/Ali Jarekji
Talla

Ministocin wato Michèle Alliot-Marie da Dominique de Villepin da kuma Michel Barnier, ana zargin cewa dagangan suka bayar da umurnin sallamar mutanen wadanda suka kaddamar da harin kan barikin Sojin na Faransa.

Harin wanda mutanen suka kaddamar a barikin Sojin na Faransa da ke birnin Bouake cikin shekarar 2004 ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Faransa 9 ba ya ga wani farar hula daya ba’Amurke da ya rasa ransa.

Tuni dai kotun yayin zamanta na yammacin jiya Alhamis ta wanke mutanen 3 wadanda ta ce basu da masaniya kan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.