Shugaba yankin Cataloniya, ya bukaci gwamnatin Spain, ta buda tattaunawa da yan aware
Dubun-dubatar masu zanga zanga ne a yau assabar 19 ga watan Okotoba 2019 ne, suka gudanar da taron gangami a birnin Barcelone na kasar Spaniya, a rana ta 5 ta soma gagarumar zanga zangar nuna rashin amincewa da hukumcin daurin da aka zartar, kan shuwagabanin yan awaren da suka yi yinkurin ballar da yankin na Kataloniya daga kasar a 2017.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tuni shugaban gwamnatin yankin na yan aware, ya yi kiran gwamnatin Spain da cewa, ba tare da gindaya sharadi ba, ta gaggauta buda shiga tattaunawa, domin magance tashe tashen hankullan da suka kazance a yankin, sakamakon hukumcin daurin gidan yari da aka zartar kan shuwagabanin na yan aware su 9.
Buraguzan duwatsu da hayakin tayyin da aka konane ya mamaye tare da kamsasa titinan Barcelona a yau assabar, bayan faruwar tashe tashen hankullan jiya juma’a da suka yi sanadiyar jikkatar mutane 180
Masu hankoron balle yankin na Katoloniya dai sun sha’ alwashin ci gaba da abinda suke yi har sai sun samu biyan bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu