Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawa na ci gaba da bore gabanin tabbatar da sabon tsarin Fansho

Yayin da ya rage kwanaki biyu gwamnatin Faransa ta fayyace sabon tsarin biyan fansho ga ma’aikatan da suka je ritaya a kasar, ko a yau litinin wani bangaren na ma’aikatan sufurin kasar na gudanar da yajin aikin don nuna rashin amincewa da wannan shiri.

Dandazon masu zanga-zanga a Faransa.
Dandazon masu zanga-zanga a Faransa. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Ko a jiya lahadi shugaba Emmanuel Macron, da firaministansa Edouard Philippe da sauran manyan kusoshin gwamnati, sun gudanar da taron gaggawa don bitar irin illolin da yajin aikin da ma’aikata suka yi a makon da ya gabata, yayin da ma’aikatan ke shirin gudanar da wani yajin aiki a gobe talata.

Tun fara wannan yajin aiki dai ba a ji ta bakin shugaba Macron ba, to sai dai Firaministansa Philippe da ke matsayin mai shiga tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago, ya ce a shirye suke su shiga tattaunawa amma zuwa yanzu bai bayyana irin sassaucin da gwamanti za ta yi ba.

A jibi labara ne firaministan zai fayyace gundarin shirin da kuma lokacin da zai fara aiki, tsarin da ma’aikatan ke adawa da shi, to sai dai kafin fayyace shirin, a yau litinin Edouard Philippe zai gana da wakilan sauran jam’iyyun siyasa da ke mara wa gwamnatin Emmanuel Macron baya.

Tuni dai sakataren kungiyar kwadagon kasar CGT Philippe Martinez ya yi gargadin cewa ma’aikata za su ci gaba da yajin aiki da shirya tarukan gangami har sai zuwa lokacin da gwamnatin ta jingine shirin baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.