An ci tarar wani dan kasar Jamus da ya kaucewa matakan kare kai daga covid 19
Gwamnatin Norway ta sanar da cin tarar wani dan Jamus da ya shiga kasar ta iyakar Netherland inda ya fara harkokinsa da jama’a ba tare da ya killace kansa na tsawon kwanaki 10 da mahukuntan kasar suka bukata ba.
Wallafawa ranar:
Mahukuntan na Norway sun bukaci mutumin ya biya tarar yuro dubu 1 da 900 baya ga haramcin shiga kasar na tsawon shekaru 2 saboda karya dokar ta kin killace kansa duk da cewa ya fito daga kasar da ke cikin jerin wadanda suka fuskanci matsananciyar cutar covid-19 da ta hallaka tarin jama’a.
Wasu daga cikin kasashen na Turai sun dukunfa yanzu haka don tattance hanyoyin da suka dace na karfafa kulawa ga mutanen da suka fito daga yankunan dake fama da cutar ta Covid 19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu