Isa ga babban shafi
Birtaniya-Faransa

Faransa da Jamus sun nemi amincewar Turai kan harajin kamfanoni na bai daya

Kasashen Faransa da Jamus sun bukaci amincewar manyan kasashen masu karfin tattalin arziki kan mafi karancin harajin da za a dorawa manyan kamfanonin duniya da zummar ganin sun samu goyan bayan sauran kasashen Turai da ke adawa da shirin.

Shugaba Emmanuel Macron da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugaba Emmanuel Macron da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. AFP - STEPHANIE LECOCQ
Talla

Matakin wanda shugaban murka joe Biden ke jagoranci na dauke da bukatar biyan kashi 15 na haraji daga cikin ribar da wadannan manyan kamfanonin duniya ke samu, matakin da ya gamu da suka daga ministan kudin Ireland.

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire yace sauyin gwamnatin da aka samu a Amurka ya bada wata dama, saboda haka ya dace su rungume ta domin amfana da ita wajen daukar mataki.

Takwaran san a kasar Jamus Olaf Scholz ya bayyana fatar ganin an kulla yarjejeniyar da zata dakile gasar da kasashen duniya keyi kan lamarin.

Scholz yace suna gab da kammala tattaunawar da zata bada damar sauya fasalin harajin manyan kamfanonin duniya.

Gwamnatin Biden a makon jiya ta bukaci amincewa da fasalin harajin bai daya na kashi 15 a tattaunawa da kungiyar hadin kan tattalin arziki da cigaba ta OECD tare da kungiyar G20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.