Akwai yiwuwar harin ta'addanci nan da sa'o'i 24-36 a Afganistan- Amurka
Kwamandojin sojin Amurka sun yi ittifakin akwai yiwuwar sake kai wani harin ta’addanci makamancin wanda aka kai a filin jirgin saman Kabul a cikin sa’o’i 24 zuwa 36 masu zuwa.
Wallafawa ranar:
Bayan da ya samu bayanai daga tawagarsa ta tsaron kasa, shugaba Joe Biden ya fada a wata sanarwa cewa harin jirgi mara matuki a kan kungiyar Khorasan ta IS da ta dauki alhakin mummunan harin Kabul ba shine na karshe ba.
Biden ya ce yanayin da ake ciki a halin yanzu yana da matukar hadari, kuma har yanzu akwai barazanar hare haren ta’addanci a filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul, yana mai cewa kwamandojinsa sun shaida masa yiwuwar hakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu