Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai-Afghanistan

Turai na laluben hanyoyin kawar da matsalar kwararar 'yan Afganistan

Ministocin harkokin wajen kasashen tarayyar Turai sun tafka muhawara kan yadda za’a shawo kan kwararar ‘yan Afghanistan da suke gujewa zama a kasar karkashin ikon Taliban.

Jagoran diflomasiyyar Tarayyar Turai, Josep Borrell, a Brussels, ranar 22 ga Maris 2021.
Jagoran diflomasiyyar Tarayyar Turai, Josep Borrell, a Brussels, ranar 22 ga Maris 2021. REUTERS - POOL
Talla

Tun bayan karbe iko daga hannun gwamnatin Ashraf Ghani da ‘yan Taliban suka yi, jama’ar kasar ke ta kwarara zuwa wasu kasashe, musamman na yankin nahiyar Turai sakamakon tsoron abinda kaje ya zo.

Muhawarar wadda Jamus ta jagoranta na da nufin lalubo hanyoyin da za’a bi wajen kare kasashen da ke karbar ‘yan gudun hijirar Afghanistan daga batagarin da ke buya a cikin su.

Haka kuma taron ya mayar da hankali kan tallafa wa kasashen da ke karbar bakuncin ‘yan kasar Afghnanistan don samun damar daukar nauyin su.

Dawowar Taliban kan mulkin Afghanistan dai ya tayar da hankalin jam’ar kasar wadanda suka rika Tururuwa a filin jirgin saman Kabul don gujewa mulkin Taliban.

Manufar taron itace samarwa da ‘yan gudun hijirar da suka isa kasashen Turai guraren zama da kuma ingantacciyar rayuwa zuwa yadda za’a ga kamun ludayin Taliban inji Ministan cikin gidan Jamus Horst Seehofer.

A cewar sa dama Jamus na cikin kasashen da ke karbar ‘yan gudun hijirar wadanda ke barin kasashen su saboda rikice-rikice, inda ya ce a shekarar 2015 kadai Jamus ta karbi ‘yan gudun hijira miliyan 10 mafi yawan su daga Syria.

Seehofer ya ce tunda kasashen turai sun amince da karbar jama’ar Afghanistan to ya zama wajibi su hada kai wajen fitar da tsari na gari cikin hanzari wanda za’a yi amfani da shi wajen inganta rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.