Faransa ta harba tauraron dan adam na ayyukan soji zuwa sararin samaniya
Faransa ta harba tauraron dan adam na ayyukan soji da kuma sadarwa zuwa sararin samaniya a jiya Asabar.
Wallafawa ranar:
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da masu bibiyar lamurra suka bayyana karuwar gogayya tsakanin manyan kasashe ta fuskar karfin mallakar kimiyya a doron kasa da sararin samaniya musamman ta fuskar bunkasa karfin sojinsu.
Kumbon dake dauke da tauraron na dan adam ya tashi zuwa sararin samaniya ne daga yankin Kourou dake Guyana, wanda zai baiwa sojojin Faransa da aka tura zuwa kusurwoyi hudu na duniya damar sadarwa cikin sauri da cikakken tsaro.
Bayanai sun ce kwararru sun kammala aikin daidaita tauraron na dan adam din na Faransa zuwa inda aka harba shi ne cikin mintuna 38 da dakika 41.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu