An gudanar da zanga-zangar adawa da sabbin dokokin korona a Turai da Austiraliya
Dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar a biranen Turai da Austiraliya sakamakon adawa da sabbin matakan kariya daga cutar korona da yanzu haka ke kara ta’azzara a wasu kasashen yankin.
Wallafawa ranar:
A kasashe da dama zanga-zanagr ta zama tarzoma kamar yadda 'Yan sandan Holand suka fuskance ta a dare na biyu, a wannan karon a birnin The Hague -- bayan tashin hankalin da aka yi daren Asabar a birnin Rotterdam mai tashar jiragen ruwa.
Netherlands
Rikici ya barke bayan wata zanga-zangar lumana a kasar Netherlands, inda masu tarzoma suka rika jifan 'yan sanda da duwatsu da kuma wutar aci-bal-bal tare da kona kekuna, inda aka kama dama daga cikinsu.
Bayan da Kasar ta Netherlands ta sake kafa dokar kulle ta makonni uku ranar Asabar, yayin da yanzu haka take shirin hana mutanen da ba su karbi allurar rigakafin cutar ba shiga wasu wurare.
Ta'azzarar cutar korona
Kashashen Turai da dama na fuskantar tsanantar cutar ta Covid 19, Inda da yawa suka tsaurara matakan hana zirga-zirga, kamar yadda Austria a ranar Juma'a ta sanya takaiceceyar dokar kulle a fadin kasar – mataki mafi girman da aka gani baya-bayan nan a Yammacin Turai.
Brussels
Tashin hankali ya barke a wata zanga-zangar adawa da matakan yaki da cutar korona a kasar Brussels, inda 'yan sanda suka ce dubbun mutane suka halarta.
An fara tattakin cikin lumana amma daga baya ‘yan sanda sun harba ruwan zafi da kuma hayaki mai sa hawaye a matsayin martani ga gungun mahalarta zanga-zanagr da suke jefa wutar aci balbal, kamar yadda wani mai daukar hoto na AFP ya shaida.
Sauran kasashe da aka yi zanga-zangar
A Amsterdam dubban mutane dake adawa da sabbin matakan sun gudanar da zanga-zanga, yayin da aka gudanar da makamaiciyar zanga-zanga a kudancin birnin Breda da ke kusa da kan iyakar kasar Belgium, da Croatia da kuma Denmark.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu