Isa ga babban shafi
Faransa-Corona

Ba mu da shirin sanya dokar kulle duk da karuwar masu corona- Faransa

Faransa ta yi ikirarin cewa ba ta da shirin dawo da dokar kulle duk da karuwar alkaluman wadanda ke kamuwa da cutar corona, sai dai za ta yi taka tsan-tsan tare da karfafa shirin wayar da kan jama'a da kuma inganta dokokin gwaje-gwaje don dakile yaduwar Covid-19.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. © Nigeria presidency
Talla

Kakakin gwamnatin Faransa Gabriel Attal ya ce la’akari da yadda ake samun karuwar alkaluman masu kamuwa da cutar ta covid-19, musamman bayan alkaluman makon jiya da aka samu sabbin kamuwa da akalla kashi 50 cikin dari, gwamnati ta sanya matakai tare da sake zage damtse don wayar da kan jama'a.

Gabriel Attal ya bayyana cewa duk da karuwar alkaluman masu kamuwa da corona a baya-bayan nan dubi da yawan mutanen da ke ci gab da karbar rigakafin cutar zai karfafa gwiwar jama'a duk da cewa dai akwai bukatar daukar matakai da kuma yin taka-tsan-tsan daga bangaren jama'a.

Gabriel Attal ya ce babu wani dalili da zai hana amanna da yiwuwar bukukuwan karshen shekara da ke tunkarowa su iya haifar da mummunar illa matukar baya sanya dokoki ba, kamar yadda aka samar yayin bikin sabuwar shekara a 2020.

Kakakin gwamnatin ta Faransa ya kuma bayyana cewa yanzu haka ana samun ci gaba a shirin rigakafin kasar ke yiwa jama'a ko da ya ke sai a watan Disamba mai zuwa mutanen da shekarunsu ya kai 50 za su fara karbar allurar ta biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.