Isa ga babban shafi

Birtaniya za ta soma killace duk wani bako da ya ziyarci kasar

Gwamnatin Birtaniya tace daga yanzu duk wani bako da ya ziyarci kasar zai killace kan sa har sai ya gabatar da shaidar dake nuna cewar baya dauke da cutar korona, sakamakon samun sabon nau’in cutar da ake kira Omicron.

Kwayar cutar Omicron,
Kwayar cutar Omicron, © via REUTERS - Social Media
Talla

Firaministan kasar Boris Johnson ya bayyana haka ga manema labarai, sa’oi bayan an gano mutane biyu na dauke da sabon nau’in cutar wadda aka ce ta samo asali daga Afirka ta Kudu.

Borris Johnson Firaministan Birtaniya
Borris Johnson Firaministan Birtaniya Tobias SCHWARZ / AFP

Tuni kasashen duniya da dama suka sanar da daukar matakan da suka hada da hana bakin da suka fito daga yankin kudancin Afirka shiga cikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.