Faransa za ta tilastawa kananan yara sanya takunkumi saboda Corona
Cikin sabbin dokokin yaki da covid-19 da Faransa za ta fara amfani da su sakamakon tsanantar cutar hatta kananan yara daga shekara 6 zuwa sama za su fara amfani da takunkumin hanci, dokar da za ta fara aiki daga litinin mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Kafin yanzu Faransa na tilastawa yara ‘yan shekaru 11 zuwa sama ne kadai amfani da takunkumin amma mahukuntan kasar sun ce karuwar alkaluman masu harbuwa a kowacce rana ya tilasta daukar matakin.
Sai dai karuwar alkaluman masu harbuwa da Corona ya tilasta kasar daukar wannan mataki kamar yadda ma;aikatar lafiya ta sanar.
karkashin dokokin daga yanzu dukkanin yaron da shekarunsa suka kai 6 ba zai samu izinin shiga tsakar jama'a ko kuma motocin haya ba har ma da makarantu face suna sanye da takunkumin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu