Isa ga babban shafi
Faransa - Coronavirus

Gargadin Macron kan rigakafin covid-19 ya haddasa yamutsi a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fusata abokan hamayyarsa gami da janyo hargitsi a majalisar dokokin kasar, biyo bayan gargadin da ya yiwa wadanda basu karbi allurar rigakafin Korona ba, inda ya sha alwashin hana su amfana da muhimman bangarorin rayuwa, tare da bayyana jin dadin ganin ya takura musu.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Macron wanda har yanzu bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a watan Afrilu ba, ya fuskanci caccaka daga abokan hamayyarsa a takarar zaben shugabancin Faransa ne, bayan hirar da yayi da Jaridar ‘Le Parisien’ inda ya ce yana matukar son ya bata ran mutanen da suka ki karbar allurar rigakafin Korona ta hanyar kayyade walwalarsu ta yau da kullum a cikin al’umma, inda sabbin dokokin dakile yaduwar cutar ta Korona za ta hana su shiga gidajen cin abinci da, wuraren shan shayi, filayen wasan da kuna gidajen Sinima, dokar da za ta fara aiki daga 15 ga watan Janairun da muke.

Tuni dai muhawarar 'yan majalisar dokokin Faransa ta yi zafin da ya sanya ‘yan adawa tilasta dakatar da muhawarar neman amincewa da kunshin dokar tsaurara matakan yaki da annobar Korona a kasar.

Daga bangaren masu neman shugabancin Faransa kuwa wadanda suka bayyana kalaman Macron a matsayin wuce gona da iri, ‘Yar takarar jam’iyyar Republican Valerie Pecresse, wacce mutane da yawa ke ganin ita ce babbar abokiyar hamayyar shugaban, ta shaida wa kafar yada labarai ta CNews cewa, Macron din bashi da ikon tantance Faransawa nagari da baragurbi.

Ita kuwa 'yar takarar shugaban kasa mai tsatsauran ra'ayi Marine Le Pen cewa ta yi, Emmanuel Macron bai taba jin kansa a matsayin shugaban dukkan Faransawa ba, yayin da Jean-Luc Malenchon da dan takara mai ra’ayin kishin kasa ya bayyana shirin tsaurara dokar yaki da Koronar a matsayin hukuncin tauye ‘yancin rayuwar jama’a.

Kididdigar da gwamnatin Faransa ta fitar a baya bayan nan dai, ta bayyana cewar kashi 91 cikin 100 na Faransawa da suka haura shekaru 18 sun samu yin cikakkiyar allurar rigakafin Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.