Isa ga babban shafi
Corona-Faransa

Faransawa na zanga-zangar adawa da tsaurara dokokin kariya daga corona

Dubban mutane ne suka fito zanga-zanga a biranen Faransa a karshen makon da ya  gabata, don nuna adawa da tsauraran matakan hana walwala kan wadanda ba su karbi rigakafin cutar Covid-19 ba, a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawwara a majalisar dokoki a kan kudirin dokar hana walwala.

Masu zanga-zanga a Faransa.
Masu zanga-zanga a Faransa. AP - Daniel Cole
Talla

A birnin Paris,  a hasumiyar Eiffel aka yi taron masu zanga-zanga mafi girma inda masu zanga zangar ke rike da tutocin Faransa da na yankunasu, tare da kwalayen da ke dauke sakonnin adawa da rigakafi da kuma takardar izinin shiga wurare ga wadanda ba su karba ba.

Wasu masu zanga zangar sun yi ta tuni ne da zanga-zangar masu sanye da riga mai launin ruwan kwai da aka yi daga shekarar 2018 zuwa 19, na adawa da zargin cewa shugaba Emmanuel Macron yana daure wa masu hannu da shuni gindi, a yayin da aka gudanar da sauran wasu tarukan a birane kamar su Bordeaux, Toulouse da Lille.

Akasarin masu zanga zangar sun yi ta rera wakokin nuna rashin amincewa da rigakafin Covid-19, ko kuma yanci ga Djokovic, shahararren dan kwallon Tennis na duniya, wanda gwamnatin Australia ta hana shi shiga gasar Australian Open ba tare da an yi mai rigakafi ba.

Sama da mutane miliyan 5 da dubu dari 5 ne wannan cuta ta kashe a fadin duniya tun da ta bulla a birnin Wuhan n akasar China a shekarar 2019 kamar yadda alkalumman kamfanin dillancin labaran Faransa ya nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.