Isa ga babban shafi
EU-Malta

Mai ra'ayin rikau ta karbi shugabancin Majalisar Tarayyar Turai

'Yan majalisar dokokin Tarayyar Turai sun zabi 'yar siyasar Malta mai ra'ayin rikau, Roberta Metsola a matsayin sabuwar shugabar Majalisar Tarayyar Turai, duk da cece-ku-ce kan fafutukar da takeyi na yaki da matsalar zub da ciki.

Sabuwar shugabar Majalisar EU Roberta Metsola 'yar kasar malta mai ra'ayin rikau.
Sabuwar shugabar Majalisar EU Roberta Metsola 'yar kasar malta mai ra'ayin rikau. AFP - PATRICK HERTZOG
Talla

Metsola ta samu gagarumin rinjaye da kuri'u 458, inda ta zama mace ta uku da ta shugabanci majalisar bayan wata yarjejeniya tsakanin manyan kungiyoyin siyasa.

Zaben nata ya zo ne mako guda bayan mutuwar shugaban majalisar dokokin EU David Sassoli, wanda dama ke dab da sauka daga mukaminsa bisa yarjejeniyar raba madafun iko.

Sabuwar shugabar ta dauki kanta a matsayin mai goyon bayan daidaiton jinsi da kuma rajin da take yi na kare hakkin mata amma kuma zafafa matsayarta na yakar zubar da ciki ya janyo suka daga abokan hamayya.

Zubar da ciki haramun ne a Malta, kasar da yawancin al’ummarta ke bin darikar Katolika kuma ko a watan Yunin da ya wuce, Metsola ta kada kuri'ar rashin amincewa da wani rahoto da ya bukaci dukkan kasashe mambobin EU su halasta zub da ciki.

Da take ajawabi a zauren majalisar, Roberata Metsola, ta ce za a bawa shirin yaki da matsalar sauyin yanayi a Majalisar Tarayyar Turai fifiko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.