Isa ga babban shafi
Ukraine

Zelensky ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su bi sahun Birtaniya

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su bi sahun Birtaniya wajen ba da taimakon soji ga kasarsa tare da kakabawa Rasha takunkumi bayan ziyarar bazata da Firayim Minista Boris Johnson ya kai Kyiv.

Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson da shugaban kasar Ukrainien Volodymyr Zelensky a Kiev, a ranar 9 ga Afrilu 2022.
Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson da shugaban kasar Ukrainien Volodymyr Zelensky a Kiev, a ranar 9 ga Afrilu 2022. AP
Talla

Birtaniya za ta bai wa Ukraine taimakon motocin yaki na igwa har 120 da makamai masu tarwatsa jiragen ruwa da na harbo jiragen sama baya ga tallafin kudi.

Fadar gwamnatin Birtaniya Downing Street ta sanar da haka bayan ziyarar bazata da Boris Jonson ya kai wa Shugaban Ukraine Volodymr Zelensky a Kyiv.

Kazamin gumurzu

A halin da ake ciki, Jami'ai a Kyiv suka ce sojojin Ukraine na shirin wani "gagarumin gumurzu da dakarun Moscow a gabashin kasar, yayin da dubban fararen hula ke tserewa saboda fargabar farmakin da Rasha ke shirin kaiwa.

A ranar Asabar ne aka dawo da kwashe mutane daga Kramatorsk da ke gabashin Ukraine, inda wani hari da makami mai linzami ya kashe mutane 52 a tashar jirgin kasa kwana daya da ta wuce, yayin da Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson ya zama shugaban yammacin Turai na karshe da ya ziyarci Kyiv.

Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson da shugaban kasar Ukrainien Volodymyr Zelensky a Kiev, a ranar 9 ga Afrilu 2022.
Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson da shugaban kasar Ukrainien Volodymyr Zelensky a Kiev, a ranar 9 ga Afrilu 2022. AP

Da yake yabawa matakin da kasar ta dauka kan mamayar Rasha, Johnson ya bai wa Ukraine motoci masu sulke da makami mai linzami don taimakawa wajen tabbatar da cewa, "ba za a sake mamaye kasar ba".

Ukraine na shirin soma kaiwa Rasha hari

Tayin nasa ya zo ne bayan shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya ce Kyiv na shirin kai wa Rasha hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.