Isa ga babban shafi

Partygate-Boris Johnson ya aikata abin kunya

Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya amsa laifin karya dokar hana fita ta hanyar halartar wani bikin rawa a fadar gwamnatin kasar a daidai lokacin da dokar hana zirga zirga ke aiki domin dakile yaduwar cutar Korona.

Firaministan Birtaniya  Boris Johnson a zauren majalisa
Firaministan Birtaniya Boris Johnson a zauren majalisa AP - Jessica Taylor
Talla

Matakin na Fira Minista Johnson ya biyo bayan fitar da wani rahoto na cikin gida kan abin kunyar da ya aikata da ake kira da “Partygate”.

Kawo yanzu dai Fira Ministan na Birtaniya bai nuna alamun sauraron kiraye-kirayen da masu suka ke yin a yayi murabus ba, saboda abinda ya aikata.Yan adawa sun bukaci Boris Johnson ya sauka daga mukaminsa.

Boris Johnson da Korona

A lokacin bullar cutar ta Korona,FiraMinistan Birtaniya ya kasance a asibiti na wani lokaci,Gwamnatin Birtaniya ta sanar da sallamar Firaminista Boris Johnson daga asibiti mako guda bayan an kwantar da shi sakamakon kamuwa da cutar Korona, wadda ta kai ga ajiye  shi a gobe da nisa na kwanaki 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.