Isa ga babban shafi

Firanministan Birtaniya Boris Johnson ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyarsa

Firanministan Birtaniya Boris Johnson ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar Conservative, matakin da zai share fagen zaben sabon firaminista bayan da ministoci da dama suka yi murabus daga gwamnatinsa da ke fama da rikici.

Firanministan Birtaniya Boris Johnson,26 ga watan Janairun 2021.
Firanministan Birtaniya Boris Johnson,26 ga watan Janairun 2021. AFP - JUSTIN TALLIS
Talla

Dayake gabatar da jawabin murabus din nasa a lamba 10 Downing Street, mista Johnson yace “yanzu a bayyane yake jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya zata fara laluben sabon shugaban jam'iyyar da zai kaiga  sabon Firayim Minista."

Boris Johnson, mai shekaru 58, ya sanar da cewa zai sauka daga mukaminsa bayan manyan-manyan tawagarsa suke ta yin murabus domin nuna adawa da shugabancinsa,  amma zai ci gaba da zama a matsayin firaminista har sai an samu wanda zai maye gurbinsa.

Zaben sabon shugaban jam'iyya

Minsta Johnson yace a mako mai zuwa za a sanar da jadawalin tseren shugabancin Jam’iyyar, bayan shekaru uku na mulkinsa da batutuwan Brexit da annobar korona kuma cece-kuce da ki taki cinyewa kan Kazafi suka mamaye.

Za a gudanar da zaben shugabannin ne a lokacin bazara kuma wanda ya yi nasara zai maye gurbin Johnson yayin taron jam’iyyar na shekara-shekara a farkon watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.