Isa ga babban shafi

Hauhawar farashin kayayyaki na barazana ga kasuwanci a kasashen G20

Wani bincike ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki, da matsalar bashi da kuma tsadar rayuwa, na haifar da babbar barazana ga harkokin kasuwanci ga kasashen G20 masu karfin tattalin arziki nan da shekaru biyu masu zuwa.

Ministan kudin Indonesia Sri Mulyani Indrawati, tana gaisawa da sakariyar baaitulmalin amurka Janet Yellen a taron G20.
Ministan kudin Indonesia Sri Mulyani Indrawati, tana gaisawa da sakariyar baaitulmalin amurka Janet Yellen a taron G20. AP - MADE NAGI
Talla

Binciken Cibiyar Tattalin Arziki ta Duniya ya gano cewa, Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa matakin da ba a taɓa gani ba cikin shekaru da dama, lamarin da ya sa kashi ɗaya bisa uku na ƙasashen G20 suka fahimci matsalar a matsayin babban abin da ke damun su.

Ko da yake manyan bankunan a faɗin duniya sun fara aiwatar da tsauraran manufofin na daidaita hauhawar farashin kayayyaki wanda hakan ke jefa duniya cikin koma baya.

Yakin Rasha da Ukraine da aka fara a faron wannan shekarar, wanda ya janyo matsalar karancin makamashi na daga cikin abubuwan da suka haddasa hauhawar farashin kayayyaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.