Isa ga babban shafi

Putin ba zai halarci taron shugabannin kasahen G20 ba

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ba zai halarci taron shugabannin kasashen G20 da za a yi a tsibirin Bali na Indonesia a mako mai zuwa ba, kamar yadda ofishin jakadancin Rashar a Indonesia ya shaida wa kamfanin dillancin laabaran Faransa.

Shugabaan Rasha Vladimir Putin.
Shugabaan Rasha Vladimir Putin. © Sergei Guneyev / AP
Talla

Babbar jami'ar ofishin jakadancin Rasha a Indonesiya Yulia Tomskaya ta ce, ba ta da tabbas ko ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov zai jagoranci tawagar Rasha zuwa G20, sannan ko Putin zai halarci taron, sai dai ta hoton bidiyo ne.

Wannan mataki ya biyo bayan cece kuceda ake ta yi a game da ko Putin zai samu halartar wanna taro da za yi a kasar Indonesi a ranakun 15 da 16 na wataan Nuwamba.

Wata majiya da ke da masaniya a game da shirin da Rasha ke yi a kan taron G20 na bana ta tabbaatar da cewa minister harkokin wajen kasar Sergie Lavrov ne zai wakilci Putin a taron.

Tuni Biden, wanda ya bayyana Putin a matsayin mai aikata laifukan yaki ya ce bashi da niyyar ganawa da Putin ko sun hadu a wajen taron, said dai idan gaanawar ta shafi batu. sakin Amurkawa da ya garkame a kasarsa.

Shugaban Indonesia, Joko Widodo ya gayyaci putin zuwa wannan taro duk kuwa da maamayar Ukraine da ya yi wada taa janyo caccakaa daga kasashen yaammacin Turai, inda a watann Agusta Widodo ya ce Putin ya amsa gayyatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.