Isa ga babban shafi

Rasha tace sojojinta na wani atisaye na musamman a Belarus

Rasha ta ce sojojinta na gudanar da wani atisayen dabaru na musamman a Belarus, a daidai lokacin da ake fargabar cewa Moscow na matsa wa kawayenta lamba don shiga yakin Ukraine.

Wani sojin Rasha yayin wani atisaye a Belarus. 2/02/22
Wani sojin Rasha yayin wani atisaye a Belarus. 2/02/22 AP
Talla

Belarus dai ta ce ba za ta shiga yakin Ukraine ba, amma a baya shugaban kasar Alexander Lukashenko ya ba da umarnin tura sojoji tare da dakarun Rasha zuwa kusa da kan iyakar Ukraine, saboda barazanar da Kyiv da kasashen Yamma ke yi.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar ta ce, "sojojin ta na gundumar Yamma...na wani aikin horo kan yaki da ta'addanci a Jamhuriyar Belarus." Ba tare ba rana.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya aike da sojoji zuwa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu a wani abin da ya kira "aikin soji na musamman i", wanda ya haifar da rikici mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

Putin ya ce yana kare masu magana da harshen Rashanci a gabashi da kudancin Ukraine kuma ya kira yakin a matsayin wani lokaci mai muhimmaci, saboda yadda dakarun kasar suka tsaya tsayin daka kan kasashen yamma da ya kira masu girman kai da suka shafe shekaru da dama suna wulakanta su tun bayan faduwar Tarayyar Soviet a shekarar 1991.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.