Isa ga babban shafi

Al'ummar Cote D'Ivoire kada ku yi amfani da farfagandar Rasha ta nuna kyamar Faransa

Ministar harakokin wajen Faransa Catherine Colonna a jiya asabar ta bukaci al'ummar Ivory Coast da kada su yi amfani da farfagandar Rasha wacce ke kara nuna kyama ga Faransawa a Afirka.Yayin da ta ziyarci Abidjan a ranakun Juma'a da asabar, Catherine Colonna ta amsa wasu daga cikin  tambayoyi game da matakan da Faransa ta dauka na yaki da labaran karya.

Catherine Colonna ,Ministar Harakokin wajen Faransa
Catherine Colonna ,Ministar Harakokin wajen Faransa © رویترز
Talla

Ministar harakokin wajen Faransa Catherine Colonna ta kara da cewa"Idan hakan ta faru, saboda akwai dakarun da ke aiki suna gaya muku shirme.

Ta kara da cewa "Ya zama wajibi mu goyi bayan ci gaban kasar nan, wajibi ne kada a dauke ku a matsayin wawaye."

Ta dage cewa Faransa a shirye ta ke ta ci gaba da ba da goyon baya ga ci gaban kasar da kuma hada matasa da ta bayyana su a matsayin masu kishi da basira.

"Muna taimakon jama'a amma muna rokonsu da su bude idanunsu su gane wanda ke taimakawa da wanda ke cutarwa," kalaman Catherine Colonna.

Ministar harakokin wajen Faransa ta sake nanata a jiya Asabar cewa Faransa na yin duk mai yiwuwa don ganin an sako Olivier Dubois, wanda aka yi garkuwa da shi a Mali, yayin da aka sako wani dan kasar Jamus da aka yi garkuwa da shi a Nijar.

Catherine Colonna a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, a gefen ziyarar da ta kai Abidjan, a Cote d'Ivoire, ta tuna cewa Olivier Dubois ya na hannun masu garkuwa da shi na tsawon watanni 20 bayan sace shi a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.