Isa ga babban shafi

An kama matashin dan bindiga da ya kashe mutane 8 a kasar Serbia

'Yan sandan Serbia sun sanar da nasarar kama matashin da ake zargi da kashe mutane takwas tare da raunata akalla 14 a wani hari na biyu da aka yi a kasar a cikin wannan mako, bayan da suka kwashe dare suna farautar sa.

'Yan sandan Serbia bayan harin mai uwa da wabi da wani dan bindiga yakai tare da kashe mutane 8 a yankin balkan na kasar.05/05/23.
'Yan sandan Serbia bayan harin mai uwa da wabi da wani dan bindiga yakai tare da kashe mutane 8 a yankin balkan na kasar.05/05/23. AP - Armin Durgut
Talla

Sa'o'i kadan kafin hakan, rundunar 'yan sanda a yankin Mladenovac mai tazarar kimanin kilomita 60 kudu da babban birnin kasar Belgrade tace tana farautar wani dan bindiga mai shekaru 21 dauke da makami mai sarrafa kansa ruwa ajallo bayan ya bude wuta daga wata mota da ke tafiya kafin ya gudu, inda nan take ya kashe mutane 8 tare da jikkata 14.

Shirin kwace makai

Shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic ya sha alwashin kaddamar da wani gagarumin shiri na kwance damarar makamai daga hannun jama'ar kasar, sakamakon karuwar masu kai hare-hare na kan mai uwa da wabi a yankin Balkan cikin wannan mako.

Shugaban ya ce shirin na da nufin kawar da daruruwan bindigogi daga hannun jama'a wanda zai hada da yin nazari sosai kan makaman da aka yiwa rajista a kasar, tare da dakile haramtattun makamai.

Yadda ake binciken motoci a Serbia bayan harin da ya kashe mutane 8 a kasar.05/05/23
Yadda ake binciken motoci a Serbia bayan harin da ya kashe mutane 8 a kasar.05/05/23 © REUTERS / ANTONIO BRONIC

Vucic ya fada a farkon makon nan cewa akwai bindigogi sama da 760,000 da aka yiwa rajista a cikin kasar mai kusan mutane miliyan 7.

Mallakar makamai

Mallakar bindigogi ya yi yawa a kasar Serbia, inda ake samun yawan kai hare-hare  duk da cewa sai an samu izini na musamman don mallakar bindigogi.

Yaƙe-yaƙe da aka yi a yankin Balkan a cikin shekarun 1990 a daidai lokacin da Yugoslavia ta wargaje sakamkon mummunar  rikicin  ya yi nasaba bazuwar makamai a kasar da makwabtantya.

Hari mafi muni

Wannan lamari na baya-bayan nan ya faru ne kasa da sa'o'i 48 bayan harin aka kai wata makaranta a wanda ke zama mafi muni a tarihin kasar Serbia, inda wani matashi dan shekaru 13 ya kashe mutane tara, ciki har da dalibai 8, a wata makaranta da ke tsakiyar birnin Belgrade ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.