Isa ga babban shafi

'Yan kasar Serbia na zanga-zangar adawa da hare-haren 'Yan bindiga

Dubun ‘yan kasar Serbia ne suka gudanar da zanga-zanga jiya Litinin, inda suka bukaci da a samar da tsaro, da hana shiryen gidajen talabijin masu haifar da tarzoma da kuma murabus din wasu manyan ministoci, kwanaki bayan wasu hare-hare biyu na harbin mai uwa da wabi ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 17.

Dubun ‘yan kasar Sabiya ne suka gudanar da zanga-zanga jiya Litinin, inda suka bukaci da a samar da tsaro, da hana shiryen gidajen talabijin masu haifar da tarzoma da kuma murabus din wasu manyan ministoci, kwanaki bayan wasu hare-hare biyu na harbin mai uwa da wabi ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 17.ranar 08 ga watan Mayu 2023
Dubun ‘yan kasar Sabiya ne suka gudanar da zanga-zanga jiya Litinin, inda suka bukaci da a samar da tsaro, da hana shiryen gidajen talabijin masu haifar da tarzoma da kuma murabus din wasu manyan ministoci, kwanaki bayan wasu hare-hare biyu na harbin mai uwa da wabi ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 17.ranar 08 ga watan Mayu 2023 AP - Darko Vojinovic
Talla

 

Al’ummar Balkan sun yi tattaki a tsakiyar Belgrade babban birnin kasar dauke da alluna da aka runu sakonnin adawa da cin zarafi, a wani yanayi da aka dade ba’a ga fitowar jama’a irin haka ba cikin shekaru da dama.

Harin 'Yan bindiga

Zanga-zangar na zuwa ne kwanaki bayan da wani dalibin makaranta dauke da bindigogi biyu ya kashe dalibai takwas da wani mai gadi, yayin da wasu dalibai shida da malami daya suka samu raunuka a Larabar da ta gabata.

Kwana daya tsakani, wani matashi dan shekara 21 ya yi harbi tare da kashe mutane takwas da kuma raunata wasu 14.Duk kuma sun mika wuya ga ‘yan sanda.

Shirin talabijin

Masu zanga-zangar da magoya bayan 'yan adawa sun bukaci a rufe gidajen talabijin da ake zargi da yada labaran karya da lalata.

Jam'iyyun adawa da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama na zargin shugaba Aleksandar Vucic da jam'iyyarsa mai ra'ayin rikau ta Serbian Progressive Party (SNS) da cin gashin kai, da cin zarafin 'yan jarida, cin zarafi ga abokan hamayyar siyasa, cin hanci da rashawa da alaka da masu aikata laifuka. Vucic da abokansa sun musanta zargin.

Vucic ya ce masu zanga-zangar a ranar Litinin din nan suna kokarin tilasta masa ya sauka daga mulki tare da hargitsa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.