Isa ga babban shafi

Turai ta ci tarar Facebook Euro biliyan 1 saboda satar bayanan jama'a

Hukumar da ke Bayar da Kariya ga Bayanan Jama’ar Turai, ta ci tarar kamfanin Facebook Euro biliyan 1 da miliyan 200 kan samun sa da laifin nadar bayanan kasashen Turai tare da sayar wa Amurka, lamarin da ya saba da dokokin bayar da kariya ga bayanan jama’a. 

Mark Zuckerberg, shugaban Facebook.
Mark Zuckerberg, shugaban Facebook. ASSOCIATED PRESS - Lea Suzuki
Talla

Yayin hukuncin na yau Litinin wanda Hukumar Bayar da Kariya ga Bayanan Jama’a ta Ireland DPC ta sanar a madadin kasashen Turai ta bayyana cewa hukumar kare bayanan jama’a ta tarayyar Turai EDPB ta bukaci lallai kamfanin na Facebook ko kuma Meta ya biya tarar adadin kudin na biliyan 1 da miliyan 200 a matsayin tara saboda samun sa da wannan laifi. 

Hukumar ta DPC ta samu kamfanin na Facebook ko kuma Meta da laifin nadar bayanan jama’ar tun daga shekarar 2020 wadanda ta mika ga Amurka, kuma mahukuntan kamfanin da ke shalkwatarsa a Dublin sun gaza bayar da cikakken bayani game da hadari da kuma take hakkin da ke tattare da aika-aikar kamar yadda kotun Turai ta bukata a baya. 

Tuni dai kamfanin na Meta ko kuma Facebook da aka fi sanin sa da shi, ya yi kakkausar suka kan wannan hukunci wanda ya bayyana da nuna masa wariya tsakanin takwarorinsa na  kamfanonin sada zumunta da dukkaninsu ke nadar bayanai.   

Shugaban sashen hulda da jama’a na Meta Nick Clegg ya bayyana cewa za su daukaka kara game da hukuncin yana mai cewa, babu wani batu mai kama da nadar bayanai da kamfanin ya yi a baya-bayan nan. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.