Isa ga babban shafi

Farfesa ya yi gwajin magani mafi girma a Faransa ba tare da izinin hukuma ba

Kungiyoyin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya a Faransa sun bukaci da a hukunta Farfesa Didier Raoult, wani likita kuma fitaccen mai bincike kan sha’anin lafiya a kasar, bayan samunsa da laifin gudanar da haramtaccen gwajin magani mafi girma ba tare da izinin gwamnati ba

Farfesa Didier Raoult, wani likita kuma fitaccen mai bincike kan sha’anin lafiya da dakile yaduwar cutuka a Faransa.
Farfesa Didier Raoult, wani likita kuma fitaccen mai bincike kan sha’anin lafiya da dakile yaduwar cutuka a Faransa. © Gerard Julien, AFP
Talla

Bayanai sun ce likitan ya rika yin amfani ne da maganin hydroxychloroquine domin gwajin warkar da wadanda suka kamu da cutar Korona.

Bincike dai ya nuna cewar Raoult, ya rika bai wa masu Korona maganin na hydroxychloroquine tsawon fiye da shekara guda, bayan da binciken kwararru ya tabbatar da cewa ba shi da wani tasiri akan cutar.

Idan za a iya tunawa dai a farkon barkewar annobar daga karshen 2019 zuwa farkon shekarar 2020, shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Brazil Jair Bolsonaro suka rika karfafawa mutane gwiwar su rika amfani da maganin Malaria na hydroxychloroquine wajen kawar da cutar ta Korona, da’awar da Didier Raoult na Faransa ya karfafa.

A watan Maris da ya gabata, likitan ya fitar da alkaluman da ke nuna cewar ya samu nasarar warkar da mutane fiye da dubu 30,000 da suka kamu da cutar Korona, sai dai har yanzu kwararru basu tantance sahihancin rahoton ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.