Isa ga babban shafi

Shugabannin Afrika na ganawa da Putin a Moscow

Tawagar shugabannin Afrika karkashin jagorancin shugaban kasar Afirka ta Kudu sun isa birnin Saint Petersburg na kasar Rasha, a kokarin shiga tsakanin da suke yi don sulhunta Kyiv da Moscow duk kuwa da kara tsamin da ruwa ke yi a tsakanin su.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran sa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran sa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa. AP - Sergei Chirikov
Talla

Shugabannin kasashen Afirka na kokarin ganin sun mika koken nahiyar su da ke fama da tabarbarewar tattalin arziki, wanda rikicin ya haifar.

Fadar shugaban Afirka ta Kudu ta ce tawagar ta Cyril Ramaphosa ta isa birnin Saint Petersburg ne bayan tattaunawar da tayi da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.

Tawagar za ta tattauna da shugaban Rasha Vladimir Putin don neman hanyar karo karshen rikicin kasashen biyu da ya kwashe tsawon watanni 16 ana yi, wanda ya gurgunta sha’anin tattalin arziki bayaga asarar rayuka da kuma rashin zaman lafiya a duniya da ya yi.

Tawagar ta kunshi shugabannin Afrika ta Kudu Ramaphosa da Macky Sall na Senegal da Hakainde Hichilema na Zambia da kuma Azali Assoumani na Comoros, wanda kuma ke shugabantar kungiyar Tarayyar Afirka AU.

Shugabannin kasashen Uganda, Masar da Congo-Brazzaville ba su sami damar kai ziyarar ba, sai dai sun tura wakilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.