Tan dubu 34 na takin Najeriya ya makale a iyakokin Turai - Lavrov
Gwamnatin Rasha ta ce akwai tan dubu 34 na takin zamani da ta aiko wa Najeriya, sai dai kuma sun makale a gabar ruwan Turai.
Wallafawa ranar:
Da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran kasar Rasha, ministan harkokin wajen kasar Sergie Lavrov a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akwai takin zamani fiye da tan dubu 260 da Rasha ta baiwa wasu kasashen duniya amma suke makale a iyakokin kasashen Turai.
A cewar sa, duk wannan takin kyauta ne kasar za ta baiwa kasashen Africa da suka hadar da Malawi, Kenya da kuma Najeriya, amma batun rashin jituwar da ke tsakanin kasar da kasashen Turai ne dakile wannan yunkuri.
Tan dubu 34 na takin zamanin dai-dai yake da buhu dubu 680.
Tun bayan kaddamar da farmakin da Rasha ta yi a Ukraine, kasar ke fuskantar takunkumi daban daban, ciki harda dakatar da ita wajen fitar da kayayyakin da take sarrafawa kasashen waje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu