Isa ga babban shafi

Wani dalibin jami'a ya bude wuta kan mai uwa da wabi

Wani dan bindiga ya kashe akalla mutane 15 tare da raunata gommai a wata jami'a da ke tsakiyar birnin Prague kafin jami'an 'yan sanda su kashe shi kamar yadda hukumomi suka bayyana.

An girke jami'an 'yan sanda a wurin da aka kai harin.
An girke jami'an 'yan sanda a wurin da aka kai harin. AP - Petr David Josek
Talla

Rundunar 'yan sanda ta bayyana maharin a matsayin dalibi a sashen koyar da wasan kwaikwayo na Jami'ar Charles.

Magajin Birnin Prague, Bohuslav Svoboda ya ce, an jibge jami'an 'yan sanda a wurin da harin ya auku a dandalin Jan Palach, yayin da aka yi kira ga mutanen da ke rayuwa a wurin da su fice tare da zama a cikin gida.

Ministan Cikin Gidan Jamhuriyar Czech, Vit Rakusan ya ce, babu wani maharin da ya saura a dandalin farmakin, yana mai kira ga jama'a da su bai wa jami'an 'yan sanda goyon baya.

Rakusan ya kuma ce, harin na bindiga ba shi da alaka da ta'addanci.

Babu wata alama da ke nuna cewa, wannan harin na da nasaba da ta'addancin kasa da kasa.

Masu aikin ceto na Prague sun tabbatar da mutuwar mutane 15 da suka hada da shi kansa maharin, yayin da wasu 30 suka samu mabanbantan raunuka.

Wani mutun da ya shaida lamarin mai suna, Pavel Nedoma ya shaida wa gidan talabijin na kasa cewa, ya ga wani maharin na bude wuta kan gadar Manes daga tsallaken Kogin Vltava.

Prime Minister Petr Fiala canceled his scheduled events and was heading for Prague.

Tuni Firaministan kasar, Petr Fiala ya soke harkokinsu da aka tsara zai gudanar da su, inda ya kama hanyar zuwa Prague. 

A wani sakon dandalin X, shugaban Czech Petr Pavel wanda ke kammala ziyara a birnin Paris ya ce, ya kadu da harin bindigar, yana mai aikewa da sakonsa na ta'aziyya ga iyalan mutanen da lamarin yaa rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.