Isa ga babban shafi
Marathon

Tsoho mai shekaru 101 ya yi ritaya daga tseren gudun Marathon

Fauja Singh, tsoho mai yawan shekaru 101 ya yi ritaya daga tseren gudun Marathon bayan ya haska a tseren gudun da aka gudanar a Hong Kong. Tsohon da ake kira da sunan Turbaned Tornado, ya yi gudun Kilomita 10 inda ya kwashe Sa’a daya da minti 32 da dakikoki 28 yana gudu a Hong Kong.

Dan wasan Marathon Fauja Singh a Hong Kong wanda ke da yawan shekaru 101 a Duniya
Dan wasan Marathon Fauja Singh a Hong Kong wanda ke da yawan shekaru 101 a Duniya REUTERS/Bobby Yip
Talla

“Zan tuna wannan rana, amma ba zan dai na yin gudu ba don bayar da agaji. Inji Mista Singh bayan kammala tseren gudun Marathon a Hong Kong.

A watan Afrilu ne Mista Singh zai cika shekaru 102 a Duniya.

A baya Tsohon ya yi gudun Kilomita 42 a tseren gudun Marathon da aka gudanar a London da Toronto da kuma New York.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.