Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta tuna da Yekini na Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta tuna da tsohon dan wasan Najeriya, marigayi Rasheed Yekini bayan cikarsa shekaru hudu da rasuwa.

Rashidi Yekini lokacin a cikin ragar Bulgeria bayan zira kwallon shi ta farko a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka a shekarar 1994
Rashidi Yekini lokacin a cikin ragar Bulgeria bayan zira kwallon shi ta farko a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka a shekarar 1994 Nigerian Vanguard
Talla

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Intanet, hukumar FIFA ta tuna da kwallon da Yekini ya jefa a ragar kasar Bulgaria a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Amurka a shekara ta 1994.

Wannan kwallon dai, ita ce ta farko da Najeriya ta ci a gasar cin kofin duniya, yayin da Yekini ya shiga cikin ragar yana girgizata, yana kuka domin nuna farin cikinsa na zura wannan kwallo mai cike da tarihi.

Har yanzu dai babu wani dan wasan Najeriya da ya ci wa kasar kwallayen da suka kai yawan na Rasheed Yekini, inda ya ke da kwallaye 37.

Ya dai rasu a ranar 4 ga watan mayun shekarar 2012 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Sannan ya bar duniya yana da shekaru 48 da haihuwa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.