'Yan wasan Najeriya basu da kwarewar zuwa Rasha - Eguavoen
Tsohon mai horar da tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, Augustine Eguavon, ya ce ‘yan wasan da mai horar da tawagar na yanzu Gernot Rohr ya zaba domin halartar gasar cin kofin duniya a Rasha, basu da kwarewar da ake bukata.
Wallafawa ranar:
Eguavoen ya yi tsokacin ne, a dai dai lokacin da tawagar ta Super Eagles ke fafata wasannin sada zumunci, na baya bayan nan shi ne wanda ta buga da Ingila ranar Asabar a filin wasa na Wembley, ta kuma yi rashin nasara da 2-1.
Najeriya wadda ke rukuni na D, mai kunshe da kasashen Argentina, Iceland da Croatia, zata buga wasan farko ne da Croatia, a ranar 16 ga watan Yuni.
Najeriya ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da fara samun tikitin halartar gasar cin kofin duniya a Rasha, kafin ta kai kammala wasanninta na neman cancantar halartar gasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu